ABNA24 : A cikin bayanin da gwamnatin kasar Morocco ta bayar dangane da kulla alakarta da Isra’ila, ta bayyana cewa abin da ya faru ba kulla alaka ba ne, ci gaban alaka ne tsakaninsu da Isra’ila, domin kuwa da can akwai alaka a tsakaninsu.
Gwamnatin kasar Morocco ta bi sahun kasashe uku daga cikin kasashen larabawa da suka fito fili suka bayyana kulla alakarsu da gwamnatin yahudawan Isra’ila, inda a halin yanzu ta zama ta hudu.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ne ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa ta sanya larabawa sun kulla alaka da Isra’ila a bayyane, domin hakan ya kara tabbatar da halscin Isra’ila da kuma samuwarta a yankin gabas ta tsakiya.
Koa cikin ‘yan makonin da suka gabata na gudanar da zaman tattaunawa tsakanin a cikin kasar saudiyya, tsakanin yarima mai jiran gado Muhammad Ben salman, da kuma sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo gami da firayi ministan gwamnatin yahudawan Isra’ila Benjamin Netanyu.
Amus Jaled wanda shi ne babban jami’I mai kula da cibiyar bincike a bangaren ayyukan tsaro na Isra’ila, ya bayyana cewa kasashen Morocco da Sudan sun kulla alaka da Isra’ila ne ba tare da sun samu komai daga Isra’ila ba, domin dukkanin alkawullan da aka yi musu kan hakan tsakaninsu da Amurka ne.
342/